Abu Huɗu Da Suka Kamata Ku Sani Kan Zazzaɓin Dengue Da Ya Ɓulla A Najeriya

 

Abu huɗu da suka kamata ku sani kan zazzaɓin Dengue da ya ɓulla a Najeriya











Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce ana zargin cewa mutum 71 sun kamu da cutar zazzaɓin Dengue, yayin da tuni aka tabbatar cewa mutum 13 sun harbu da ita a jihar Sokoto.

Ya zuwa ranar Litinin babu rahoton rasa rai sanadiyyar cutar a Najeriya, sai dai NCDC ta ce tana haɗa hannu da masu ruwa da tsaki domin tantance ha darin da ake ciki tare da ɗaukan mataki.

Ɓullar cutar a Najeriya na daga cikin ɓarkewar ta da ake samu a ƙasashen yammacin Afirka.

Cutar ta ɓarke a ƙasashe irin su Senegal da Burkina Faso da Cabo Verde da Chad da Habasha da Mali da Togo.

Mene ne zazzaɓin Dengue?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta lissafa zazzaɓin Dengue cikin cutuka masu barazana ga bil'adama a duniya.

Ɗaya ne daga cikin cutuka mafi saurin yaɗuwa waɗanda sauro ke haddasawa.

An bayyana cewa rabin al'ummar duniya na cikin haɗarin kamuwa da cutar.

Kamar wasu takwarorinsa, Dengue cuta ce wadda sauro, musamman macen sauro ke yaɗawa tsakanin al'umma.

Cutar ta samo asali ne daga yankin kudu maso yammacin nahiyar Asiya a ƙasashe kamar Thailand da Philippines da Vietnam da Cambodia.

Cutar ta fara ɓulla ne a shekarun 1950.

Alamomin Dengue

Kimanin kashi 80 cikin 100 na masu kamuwa da Dengue ba su sanin cewa sun kamuy da ita, kasancewar ba za ta nuna wata alama a tattare da su ba.

Wasu kuma takan nuna alamu maras tsanani, waɗanda mutum zai yi fama da su tsakanin kwana biyu zuwa bakwai.

Sai dai cutar kan tsananta a wasu mutanen, inda sukan yi fama da abubuwa kamar haka:

  • Amai mai tsanani
  • Zubar jini daga baki
  • Haɓo
  • Kumburin hanta

Da zarar aka fahimci cewa mutum na fama da waɗannan alamomi na zazzaɓin, to ya kamata a ba shi kulawa cikin gaggawa, domin kuwa suna iya kai ga mutuwa.

A asibiti ana amfani da wasu hanyoyi wajen gano mai ɗauke da cutar ta Dengue.

Ana iya maganin cutar?

Babu wani takamaiman magani da ake da shi na cutar Dengue.

Akwai wani rigakafi da aka samar, wanda ƙasashe ƙalilan ne suka amince da shi.

Sai dai babu isasshen wannan rigakafi a ƙasashen Afirka.

Ta yaya za a kare kai daga Dengue

Dakta Usman Qalbussunnah na Babban asibiti Rigasa a jihar Kaduna da ke Najeriya ya ce za a iya amfani da dabarun kauce wa kamuwa da Maleriya wajen kare kai daga kamuwa da cutar Dengue.

Ya ce "Kamar yadda kuka sani, sauro ne ke haddasa zazzaɓin Dengue, saboda haka nan yadda ake kauce wa maleriya haka ake kauce wa kamuwa da Dengue."

Wasu daga cikin hanyoyin kariya daga kamuwa da Dengue su ne:

  • Kwana a cikin gidan sauro
  • Kawar da ruwa mai kwanciya
  • Kawar da datti daga muhalli


Post a Comment

Previous Post Next Post