Rusa Zaben Abba Kabir: Jerin Hukunce-hukuncen Kotu da Suka Bai Wa Kowa Mamaki a 2023.

 Rusa Zaben Abba Kabir: Jerin Hukunce-hukuncen Kotu Da Suka Bai Wa Kowa Mamaki A 2023.



Ya kamata kotu ta zama kafar da za ta kwata wa dan Najeriya hakkinsa, amma wasu hukunce-hukuncen kotun zabe sun bai wa 'yan kasar mamaki.

. Ahmad Lawan vs Machina Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan bai yi takarar tsayawa sanatan Yobe ta Arewa ba amma an sanar da shi a Kotun koli.

Bashir Machina wanda shi ne sahihin dan takarar dole ya shiga sharia don kare kujerarshi a babbar Kotun Tarayya. Daga bisani APC da Lawan sun garzaya Kotun Koli inda suka yi nasara.

 Masana shari'a da sauran mutane sun yi Allah wadai da irin wannan hukunci da aka yanke. 2. 

Abba Kabir vs Gawuna Wani abin da yafi bai wa mutane mamaki shi ne kwace kujerar Gwamna Abba Kabir a jihar Kano. 

Kotun zabe ta rusa zaben gwamnan da kwashe kuri'u dubu 165 saboda rashin ingancinsu. Har ila yau, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin da cewa Abba ba dan jam'iyyar NNPP ba ne. 

A jiya Alhamis, Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben jihar inda yanzu ake dakon hukuncin karshe. 3. Mutfwang vs Goshwe Wani abin mamaki kuma shi ne shari'ar zaben jihar Plateau tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang da Nentawe Goshwe. 


Post a Comment

Previous Post Next Post