Sabuwa 'Yan Bindiga Sun Tashi Wani Kauyen Abuja Bayan Kashe Mutum 1 DaWata Neman Fansar N5m
Sakamakon hare-haren 'yan bindiga, mutanen kauyen Yewuti da ke babban birnin tarayya Abuja sun yi hijira zuwa makwaftan garuruwa Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun addabi garin da kai hari, inda ko a baya sai da suka kashe mutum daya da sace wasu da dama A cikin wadanda aka sace ne aka biya Naira miliyan biyar kudin fansa, cikin mutanen har da mahaifin mataimakin shugaban karamar hukumar.
FCT, Abuja - Da yawan mazauna kauyen Yewuti da ke karamar hukumar Kwali, babban birnin tarayya Abuja sun yi hijira daga garin saboda hare-haren 'yan bindiga. A baya-bayan nan ne dai 'yan bindiga suka kashe musu mutum daya tare da sako mutum hudu da suka sace bayan karbar Naira miliyan biyar da wasu kayayyaki abinci
Hare-haren 'yan bindiga a kauyen Yewuti
Rahoton birni dakuma laifi a ranar 18 ga watan Nuwamba ya nuna cewa 'yan bindiga sun farmakin kauyen tare da sace mutum 8 ciki har da mahaifin mataimakin shugaban karamar hukumar.
Sai dai a ranar 2 ga watan Disamba suka sako mutu uku ciki har da mahaifin mataimakin karamar hukumar bayan karbar Naira miliyan biyar, Chronocle ta ruwaito.
Da ya ke tabbatar da kashe dan kauyen da kuma sako sauran mutum hudu, wani daga cikin iyalan wadanda abin ya shafa ya ce an sako 'yan uwansu a yammacin ranar Juma'a.
Abin da rundunar 'yan sanda ta ce kan wannan rahoto Wani mazaunin garin, Shuaibu Aliyu, wanda ya zanta da wakilin Daily Trust a ranar Lahadi ya ce 'yan kauyen musamman mata da kananan yara sun yi hijira zuwa Awawa, Abaji da kauyen Yongoji da Kwali.