Shugaba Ahmed BolaTinubu, Zulum Da Wasu Manyan Ƙusoshi Da Zasu Halarci Gasar Karatun Alqur'ani Mai Girma.

 Shugaba Ahmed BolaTinubu, Zulum Da Wasu Manyan Ƙusoshi Da Zasu Halarci Gasar Karatun Alqur'ani Mai Girma.


Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan baƙin da ake sa ran zasu halarci gasar karatun Alkur'ani Mai Girma na ƙasa a jihar Yobe Mai Alfarma Sarkin Musulmi, 

Gwamna Zulum da takwaransa Mai Mala Buni na cikin waɗanda ake sa ran zasu halarci wurin A ranar Jumu'a 29 ga watan Disamba, 2023 za a buɗe gasar karatun ta bana a Damaturu, babbak birnin jihar Yobe.

Damaturu, jihar Yobe - Ana tsammanin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai halarci gasar karatun Alƙur'ani ta ƙasa da aka shirya yi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe. 

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na III, gwamnonin jihohin Borno da Yobe, Babagana Zulum da Mala Buni, na cikin waɗanda ake sa ran zasu halarci wurin. 

Kwamishinan ma'aikatan cikin gida, yaɗa labarai da al'adu na jihar Yobe, Abdullahi Bego, shi ne ya faɗi haka yayin hira da ƴan jarida a sakateriyar NUJ da ke Damaturu. 

Manyan mutanen da zasu halarci wurin Ya ce gasar karatun Alkur'anin da za a fara ranar Juma’a 29 ga watan Disamba zai samu shugaba Tinubu a matsayin babban bako na musamman, cewar yasu. Haka nan kuma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana.

Sai kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar wanda ake ran zai halarci wurin a matsayin uban ƙasa. 

Yayin da ministan harkokin ƴan sanda, Sanata Ibrahim Geidam, zai kasance shugaban bikin buɗe gasar karatun na littafi mai tsarki. 

A cewar Bego, kimanin mutane 296 da za su fito daga jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja ne zasu fafata a gasar mai kunshe rukunoni 10. 


Post a Comment

Previous Post Next Post